IQNA

Za A Ci Gaba Da Shari'ar Mutumin Da Ake Zargi Da Kitsa Harin 11 Ga watan Satumba A Amurka

21:21 - September 07, 2021
Lambar Labari: 3486282
Tehran (IQNA) za a ci gaba da gudanar da shari'ar Khalid Sheikh Muhammad mutumin da ake zargi da kitsa harin 11 ga watan Satumba a Amurka.

Jaridar Quds Alarabi ta bayar da rahoton cewa, za a ci gaba da gudanar da shari'ar Khalid Sheikh Muhammad mutumin da ake zargi da kitsa harin 11 ga watan Satumba 2001 a Amurka, inda Amurka ta yi iamnin cewa shi ne mutumin da ya shirya harin baki daya, tare da tsara yadda aka aiwatar da shi.

An kwashe tsawon shekaru dai ana ta bin kadun wannan shari'a, wadda aka yi ta jan kafa a kanta saboda dalilai na siyasa.

Zaman sauraren shari'ar da yake farawa daga yau 7 ga watan satumba, zai ci gaba har zuwa ranar 17 ga wannan wata, inda Khalid Sheikh Muhammad zai gurfaa, tare da Walid Muhammad saleh Mubarak, Ali Abdulaziz Ali, Ramzi Bin Shaibah, da kuma Musatafa Ahmad Adam Hausawi.

Hukumar FBI ta kasar Amurka ta sheda cewa, kusan dukkanin bayanan da ake da su na tuhumar wadannan mutanen, tabbatattun bayanai ne, domin kuwa kusan dukkanin abin da ke ciki su ne da kansu suka yi bayani, baya ga sauran abubuwa wadada suka dogara a kan bayanan sirri da kuma shedu na mutane da kuma na hotunan bidiyo da daisauransu. 

 

3995773

 

 

 

 

captcha