Shafin yada labarai na Palestine yaum ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin yahudawan sahyuniya ta sake kame 4 daga cikin Falastinawa 6 da suka kubutar da kansu daga gidan kaso a cikin wannan mako.
Bayanin ya ce tun bayan da Falastinawan suka tsere daga gidan kason, jami'an tsaron gwamnatin yahudawan suke ta farautarsu, inda suka kama dangin wasu daga cikin Falastinawa suka fice daga gidan kason.
Amma ya zuwa yanzu dai jami'an tsaron yahudawan sun iya kama hudu daga cikin Falastinawan, kuma sun sake mayar da su a gidan kaso.
A nasu bangaren kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa sun gargadi Isra'ila kan daukar duk wani mataki na taba lafiyar Falastinawan, domin taba su yana a matsayin taba dukkanin al'ummar Falastinu ne.
Yanzu haka dai akwai dubban Falastinawa da suke tsarea cikin gidajen kason yahudawan Isra'ila, mafi yawa daga cikinsu Isra'ila na zarginsu da kasancewa mambobin kungiyoyin gwagwarmaya da da mamayar ad take yi wa kasarsu ne.