IQNA

An Sanya Wani Masallaci Cikin Jerin Wurare Da Aka Gina Su Da Fasaha Ta Musamman A Burtaniya

21:42 - September 11, 2021
Lambar Labari: 3486296
Tehran (IQNA) an sanya masallacin Cambriege a cikin jerin muhimman wurare da aka yi amfani da fasaha ta musamman wajen gina su a Burtaniya.

Tashar ITV ta bayar da rahoton cewa, kwamitin kwararru na masarautar Burtaniya kan ayyukan fasaha na musamman a kasar, ya sanya babban masallacin Cambriege a cikin jerin muhimman wurare da aka yi amfani da fasaha ta musamman wajen gina su a kasar.

Rahoton ya ce, a halin yanzu wannan masallacin yana cikin wurare guda 54 aka zaba a matsayin muhimman wurare da aka yi amfani da fasaha ta musamman wajen gina su a shekara ta 2021.

Kwamitin yana bayar da kyautuka na musamman a kowace ga cibiyoyin da aka zaba domin karfafa ayyukan bunkasa al'adu da kuma fasaha a kasar.

 

 

 

3996411

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: karfafa ، musamman ، cibiyoyi ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha