IQNA

Takardun Tafsirin Kur'ani Da Aka Rubuta Fiye Da Shekaru Dubu Da Suka Gabata

14:40 - September 15, 2021
Lambar Labari: 3486311
Tehran (IQNA) dakin karatu na birnin Iskandariyya a kasar Masar na ajiye da takardun tafsirin kur'ani mafi jimawa a duniya.

Shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, dakin karatu na birnin Iskandariyya a kasar Masar na ajiye da takardun tafsirin kur'ani mafi jimawa a duniya, wanda ake kira da tafsirin Albusti, wanda Abu Ishaq Bin Ibrahim Albusti ya rubuta shi, wanda ya rasu shekara ta 307 bayan hijirar manzon Allah daga Makka zuwa Madina.

Tun daga wancan lokaci wannan tafsiri ake kula da shi shekaru bayan shekaru, wanda daga karshe dai ya isa dakin karatu na birnin Iskandariyya, wada yake dauke da littafai masu tarin yawa da aka rubuta su shekaru masu yawa da suka gabata a cikin takardu da fatunsu na asali.

Baya ga tafsirin ayoyin kur'ani, akwai hadisan ma'aiki a cikin littafin, wadanda suke bayani kan ayoyi da kuma bayanin saukarsu.

Sannan kuma an rubuta a cikin shafuka 233, kuma a cikin shafi akwai shedara 21 da tsarin rubutu da ake kira magribi.

Nadiya Al-sharif ita ce shugabar bangaren baje koli na babban dakin karatu na birnin Iskandariya, ta bayyana cewa akwai dadaddun littafai makanatan wannan da yawansu ya kai 120 a cikin wannan dakin karatu da ake adana su.

3997642

 

Abubuwan Da Ya Shafa: dakin karatu ، birnin Iskandariya ، hijirar manzon Allah ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha