IQNA

Sheikh Qasem: Ya Kamata Mahukuntan Bahrain Su Sake Tunani Kan Murkushe 'Yan Adawar Siyasa

19:30 - September 19, 2021
Lambar Labari: 3486327
Tehran (IQNA) babban malamin addini na kasar Bahrain ya kirayi mahukuntan kasar da su sake tunani kan murkushe masu adawar siyasa da suke yi.

Shafin yada labarai na Amuqawim ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayaninsa ya gabatar a jiya, babban malamin addini na kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Isa Qasem, ya kirayi mahukuntan kasar da su sake yin tunani kan matakan da suke dauka na yin amfani da mulkinsu wajen gamawa da duk wani mai sabanin ra'ayi da su.

Ya ce al'ummar kasa ita ce karfin iko, ba kujerar da mai iko yake zaune a  kanta ba, ko kuma jami'an tsaro da sojoji da soji da suke kare shi a kan wannan kujera ba.

Domin kuwa a cewar malami, duk mai mulkin da al'ummarsa ba su tare da shi, shi kansa ba zai taba jin dadin mulkin nasa ba.

A kan haka ya ce, yin aiki tare da kowane bangare na al'ummar kasa ba tare da la'akari da banbacin akida ko addini ko ra'ayin siyasa ba, shi ne zai hada kan al'ummar kasar baki daya, kuma shi ne zai ba mahukuntan kasar natsuwa, rashin hakan kuma shi ne zai sanya su zama cikin zullumi da tsoron jama'a.

 

3998436

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha