IQNA

Jagoran Juyi Na Iran Ya Yaba Wa 'Yan Wasan Kwallon Raga Na Kasar Da Suka Lashe Kofin Asia

19:31 - September 20, 2021
Lambar Labari: 3486330
Tehran (IQNA) jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran ya yabawa 'yan wasan kwallon raga na kasar da suka lashe kofin zakarun nahiyar Asia.

Shafin yanar gizo na ofishin jagora ya bayar da bayanin cewa, jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran ya yabawa 'yan wasan kwallon raga na kasar da suka lashe kofin zakarun nahiyar Asia.

A cikin matanin bayanin wanda ya zo kamar haka:

Da Sunan Allah Mai Girma

Nasarar da 'yan wasan kasar Iran suka samua  wasannin cin kofin zakarun nahiyar Asia, babban abun murna ne da farin ciki ga daukacin al'ummar kasar.

Ina mika godiya ta musamman ga dukkanin matasa 'yan wasa da suka nuna kwazo, da kuma masu horar da su har su kai ga samun wannan nasara.

 

Sayyid Ali Khamenei 

20 Satumba 2021

 

3998813

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha