IQNA

Dan Kasar Iran Ya Zo Na Daya A Gasar Kur'ani A Kasar Croatia

23:27 - September 26, 2021
Lambar Labari: 3486353
Tehran (IQNA) dan kasar Iran ya zo a mataki na farko a gasar kur'ani mai tsarki ta kasar Croatia

A ci gaba da gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasar Croatia, Saina Tabbakhi dan kasar Iran ya zo a mataki na farko a gasar.
Wannan gasar dai tana daga cikin wadanda ake gudanarwa a kasar Croatia a kowace shekara, a bangarorin harda da kuma tilawa, wanda makaranta da mahardata daga kasashe daban-daban suke halarta.
A kowace shekara makaranta da mahardata kur'ani daga kasar Iran suna halartar gasar, amma a wannan karon bangaren harda ne kawai wakilin Iran ya halarta.
Bayan amsa tambayoyi ba tare da kure ba, daga cikin surorin Nisa, Taubah, Sajdah, Waqia, Saina Tabbakhi ya zo na daya a gasar.
 
 
 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha