IQNA

Hamas Da Jihad Sun Sha Alwashin Fadada Ayyukan Gwagwarmayar Fada Da Isra'ila

23:32 - September 26, 2021
Lambar Labari: 3486354
Tehran (IQNA) Sojojin Isara’ila sun kashe Falasdinawa akalla 5 a wasu hare-haren da suka kai kan wasu garuruwan a yankin yamma da kogin Jodan.

Sojojin haramtacciyar kasar Isara’ila (HKI) sun kashe Falasdinawa akalla 5 a wasu hare-haren da suka kai kan wasu garuruwan a yankin yamma da kogin Jodan.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto kamfanin watsa labarai na WAFA na Falasdinawa na cewa sojojin yahudawan sahyoniyya sun yiwa garin Burqin kusa da birnin Qudus kawanya suka kuma shiga wani gida a garin suka kama dukkan mutanen gidan suka tafi da su.

Amma daga baya Falasdinawa a garin suka ta da bori wanda ya sa yahudawa suka bude wuta suka kashe mutane biyu daga cikinsu. Na farkon mai suna Usama Yaser Sabah dan shekara 22 a duniya ne, sannan na biyun kuma wanda ba’a bayyana sunansa ba, gawarsa ta na hannun yahudawan.

Sai kuma garin Kafr kusa da Jenin inda a namma yahudawan suka kama falasdinawa biyu a wani gidan saida mai a cikin garin.

 

4000335

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Jihad ، Hamas ، gwagwarmaya ، yahudawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha