IQNA

Tilawar Hadin Gwiwa Tsakanin Makaranci Dan Turkiya Da Dan Morocco

20:30 - September 28, 2021
Lambar Labari: 3486361
Tehran (IQNA) makanta kur'ani mai tsarki 'yan kasar Turkiya da Morocco sun gudanar da tilawa ta hadin gwiwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, makanta kur'ani mai tsarki 'yan kasar Turkiya Usman Bastanchi da dan Morocco Anas Burraq sun gudanar da tilawa ta hadin gwiwa inda suka karanta surat Qadr.

Usman Bastanchi dai haifaffen lardin Izniq na kasar Turkiya a ne a garin Borsa, kuma ya shajara da kyakkyawan sautinsa na karatun kur'ani.

Shi ma Anas Burraq yana daga cikin fitattun makaranta na kasar Morocco, wanda ya zo na uku a gasar da aka gudanar a shekarar 2014  a garin Sharija da ke hadaddiyar daular larabawa.

4000814

Abubuwan Da Ya Shafa: hadin gwiwa ، karanta ، kasar Turkiya ، kasar Morocco ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha