IQNA

Sheikh Zakzaky Ya Zanta Da Tashar PressTV A Karon Farko Tun Bayan Fitowa Daga Gidan Kaso

21:10 - September 29, 2021
Lambar Labari: 3486366
Tehran (IQNA) Sheikh Zakzaky ya yi zantawa ta farko da tashar PressTV tun bayan sakinsa daga gidan kaso.

Sheikh Ibrahim Zakzaky ya zanta da tashar PressTV wadda ita ce zantawa ta farko da wata kafar yada labarai tun bayan fitowarsa daga gidan kaso.

A yayin tattaunawar, Sheikh Zakzaky ya yi bayani kan muhimman abubuwan da suka faru da shi da kuma magoya bayan Harka Islamiyya tun daga lokacin kama shi da kuma abubuwan da suka faru a Zariya.

Ya bayyana yadda aka kashe da dama daga cikin mutanensa, da kuma yadda aka kashe 'yayansa uku a lokacin gami da 'yar uwarsa, da kuma jikkata shi tare da matarsa.

Malamin ya bayyana abin da ya faru da cewa lamari ne mai ban mamaki, domin kuwa su ba su taba kowa ba, kuma abin da suke yi na zaman lafiya, kamar yadda kuma babu wata doka ta Najeriya da ta hana hakan.

Ya kuma jaddada cewa, gwagwarmayar da yake yi ta 'yan adamtaka ce, wanda hakan yasa take da goyon baya daga bangarori daban-daban ba sai mabiya mazhabar shi'a ba.

Haka ann kuma ya yi godiya ga dukkanin wadanda suka taimaka da duk abin da za su iya a lokacin da yake tsare, da masu addu'oi gami da masu zanga-zanga, da masu bayanai da masu bin matakai na shari'a da dai sauransu.

 

4001326

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sheikh zakzaky ، gidan kaso ، zantawa ، yada labarai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha