IQNA

Musulmin Belgium Sun Kai Kara A Kotun Tarayyar Turai Kan Hana Su Yin Yanka Irin Na Musulunci

21:18 - October 02, 2021
Lambar Labari: 3486375
Tehran (IQNA) musulmin kasar Belgiium sun shigar da kara a kotun kungiyar Tarayyar Turai kan hana su gudanar da yanka irin na addinin musulunci.

Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, sakamakon hana su gudanar da yanka irin na addinin musulunci, musulmin kasar Belgiium sun shigar da kara a kotun kungiyar Tarayyar Turai.

Kutun kundin tsarin mulki ta kasar Belgium ce dai ta fitar da hukuncin, wanda ya haramta yanka dabbobi da salo irin na yanka na addinin musulunci, da sunan kare hakkin dabbobi.

Kungiyoyin musulmi a kasar Belgium baki daya sun hadu kan daukaka kara dangane da wannan hukunci, wanda suke kallonsa matsayin tauye hakkinsu na addini, domin kuwa bin tsari na yanka daddobi a wurin musulmi tsari ne na addini, wanda ya ginu a kan koyarwa ta musulunci.

A halin yanzu dai musulmin sun daukaka kara zuwa kotun Tarayyar Turai domin yin dubi a kan wannan batu.

4001768

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha