
Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa, a yau kotun Isra'ila ta fitar da hukunci da ke nuna amincewarta ga yahudawa su rika gudanar da ayyukansu an ibada a cikin masallacin Quds mai alfarma.
Baya ga haka kuma kotun ta janye hukuncin da ya haramtawa malamin yahudawa mai tsattsauran ra'ayi Aria Libo shiga cikin masallacin Quds, saboda gudanar da tarukan idin Tilmudi na yahudawa da yake yi a cikin masallacin, wanda yake kawo yamutsi tsakaninsu da Falastinawa da sauran musulmi a cikin masallacin.
Sannan kuma da koyar da yahudawa addinin yahudanci da yake yi a cikin masallacin, wanda a halin yanzu kotun ta ba shi damar yin hakan.