IQNA

Taliban Ta Ce Wadanda Suke Da Hannu A Harin Kunduz Za Su Fuskanci Hukunci Mai Tsanani

21:14 - October 09, 2021
Lambar Labari: 3486406
Tehran (IQNA) kungiyar Taliban ta ce wadanda suke da hannu a harin ta'addancin da aka kai a masallacin Juma'a a Lardin Kunduz za su fuskanci hukunci mai tsanani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kungiyar Taliban da ke rike da iko a kasar Afghanistan ta fitar a yau, ta ce wadanda suke da hannu a harin ta'addancin da aka kai a masallacin Juma'a a Lardin Kunduz za su fuskanci hukunci mai tsananin gaske.

Mai magana da yawun kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid ya bayyana cewa, abin da 'yan ta'addan Daesh suke yi a kasar Afghanistan ba abu ne da za a sanya ido a  kansa ba, dole ne a dauki kwararan matakai na shiga kafar wando daya da wadannan 'yan ta'adda.

Kungiyar Daesh dai ta ce ita ce take da alhakin kai harin na ranar Juma'a a masallacin Sayyid Abad da ke cikin gundumar Kunduz, inda wani dan ta'addan da ya yi jigidar bama-bamai ya tarwatsa kansa a tsakiyar masallata a lokacin sallar Juma'a, inda ya kashe masallata fiye da 100 tare da jikkata wasu fiye da 200.

Harin da ya fuskanci martani da Allawadai daga sassa daban-daban na duniya, da hakan ya hada da martanin Majalisar Dinkin Duniya, inda ta yi tir da harin tare da bayyana shi da cewa aiki ne na dabbanci.

Haka nan ita ma kasar Iran ta yi Allawadai da harin, tare da kiran mutanen kasar Afghanistan da su kara hada kansu domin fuskantar kalubalen da ke a gabansu.

Ita cibiyar azhar ta kasar da kuma babbar cibiyar ilimi ta Hauza da ke birnin Najaf a kasar Iraki karkashin jagorancin Ayatollah sistani, duk sun yi tir da Allawadai da wannan hari, tare da bayyana wadanda suka kai harin da cewa aikin nasu ba shi da wata alaka da addinin musulunci.

 

4003457

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha