IQNA

Jami'an Tsaron Iraki Sun Samu Nasarar Kame Mutum Na 2 A kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Daesh

16:28 - October 11, 2021
Lambar Labari: 3486411
Tehran (IQNA) jami’an leken asirin kasar Iraki sun cafke wani babban jigon kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh

Hukumomi a Iraki, sun sanar da cewa jami’an leken asirin kasar sun yi nasarar cafke wani babban jigon kungiyar Daesh, a wani samame da suka kaddamar a wajen kasar.
An cafke, Sami Jasim al-Jaburi, a wajen iyakokin Iraki, kamar yadda firaministan kasar Moustafa al-Kazimi, ya wallafa a shafinsa na tuwita.
 
Saidai bai bayyana takamaimai inda aka kama shi, amma ya ce kamun da aka yi masa na zuwa ne a daidai lokacin da ake gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na gabanin wa’adi a jiya Lahadi.
 
Sami Jasim al-Jaburi, wanda ake dangantawa da mai tallafawa kungiyar Daesh, da kudi an jima da duniya ke nemansa ruwa a jallo.
 
A cen baya dai Amurka ta sanya ladan $ miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayyani game da mutumin wanda ya taka mahimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin kudin kungiyar ta Daesh, bayan saka shi a cikin jerin ‘yan taddan data kakaba wa takunkumi.
 
Haka kuma Sami Jasim al-Jaburi, ya yi zama mukadanshin tsohon shugaban kungiyar Abou Bakr a-Baghdadi, kuma na hannun daman shugaban kungiyar ne na yanzu Abou Ibrahim al-Hashemi al-Qourachi.
 

 

4004006

 

 
Abubuwan Da Ya Shafa: dangantawa ، duniya ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha