IQNA

Za'a Nuna Al -Qur'ani Mafi Girma a Duniya a Expo 2020 Dubai wanda Aka Yi Rubutunsa Da Fasaha Ta Sassaka

Tehran (IQNA) An shirya wani sashe da za a nuna Al -Qur'ani mafi girma a duniya a Expo 2020 Dubai, wanda aka yi rubutunsa da fasaha ta sassaka.
Wannan aikin dai wani ɗan asalin ƙasar Pakistan kuma dan Canada shi ne ya aiwatar da shi mai suna Shahid Rassam, wanda ya shafe shekaru biyar yana gudanar da wannan aiki a Karachi.
 
Tsohon mazaunin UAE yanzu haka yana da ƙungiyar ƙwararrun masu zane-zane da masu zanen hoto su 200, kuma yana fatan kammala aikin Kur'ani mai fadin mita murabba'i 5 nan da shekarar 2026.
 
Shafukan suna da fadin mita 2.6 da mita 1.98, kuma idan aka kammala aikin littafin mai tsarki zai zama kwafin kur'ani mafi girma a duniya a yanzu.
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: hoto ، shekarar ، zane-zane ، kammala aikin littafin ، mai tsarki