IQNA

Azhar Ta Bukaci Taliban Da Ta Bar Mata Su Nemi Ilimi A Kasar Afghanistan

21:09 - October 12, 2021
Lambar Labari: 3486419
Tehran (IQNA) babban malamin cibiyar ilimi ta Azhar ya kirayi kungiyar Taliban da ta bar mata a Afghanistan da su nemi ilimi.

Azhar Ta Bukaci Taliban Da Ta Bar Mata Su Nemi Ilimi A Kasar AfghanistanShafin Alwafd ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani sako da ya fitar a yau, Sheikh Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar ilimi ta Azhar ya kirayi kungiyar Taliban da ta bar mata a Afghanistan da su nemi ilimi a kasar Afghanistan.

Malamin ya ce, a lokacin da musulunci ya zo ya 'yantar da mata daga jahilcin da aka sanya su, da bautar da su, da kuma mayar da su koma baya a cikin al'umma, kamar yadda kuma muslunci ya baiwa mace matsayinta a cikin rayuwa da al'umma da zamantakewa.

A kan haka Shekhul Azhar ya ce, yana kira ga kungiyar Taliban wadda take rike da madafun iko a kasar Afghanistan, da ta gaggauta janye matakin da ta dauka na hana mata zuwa makarantu domin samun ilimi.

Kungiyar Taliban dai ta hana mata halartar zuwa ajujuwan karatu a jami'oi da kuma makarantu na sakandare a fadin kasar, wanda kuma yana daya daga cikin abin da ake jin tsoron zai iya faruwa matukar Taliban ta kwace iko da Afghanistan.

 

 

4004441

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha