IQNA

Kwamitin Malamai A Aljeriya Ya Mayar Wa Shugaban Faransa Macron Da Kakkausan Martani

16:35 - October 13, 2021
Lambar Labari: 3486421
Tehran (IQNA) Kwamitin malaman addinin muslunci a kasar Aljeriya mayar wa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da kakkausan martani.

Kwamitin malaman addinin muslunci a kasar Aljeriya mayar wa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da kakkausan martani, kan furucin da ya yi dangane da mulkin mallakar Faransa a kasar.
 
Tashar TRT ta bayar da rahoton cewa, Abdulrazak Qasum shugaban kwamitin malaman addinin muslunci na kasar Aljeriya ya fitar da wani bayani a jiya, wanda ya kunshi martani mai zafi daga kwamitin Malaman, dangane da furucin da shugaba Faransa Emmanuel Macron ya yi, wanda ya bayyana cewa, tun kafin mulkin mallakar Faransa a Aljeriya, da ma kasar ta kasance karkashin mulkin mallaka.
 
Bayanin kwamitin malaman na kasar Aljeriya ya ce, idan Macron yana nufin kasar Aljeriya ta kasance karkashin daular Usmaniyya kafin zuwan Faransa ne, to Daular Usmaniyya ba mulkin mallaka suka yi wa kasar Aljeriya ba, sun shigo Aljeriya ne domin kiran mutanen kasar da su taimaka wajen yakin Salibiyya.
 
Haka nan kuma a cewar bayanin, ba su yi wa mutanen Aljeriya kisan kiyashi ba, kamar yadda kuma ba su sace dukiyar Aljeriya suka tafi da ita kasarsu ba, haka nan kuma ba su tilasta ma al’ummar Aljeriya magana da harshensu ba, sabanin abin da kasar Faransa ta aikata a kan al’ummar kasar Aljeriya.
 
A kan haka bayanin ya bayyana mulkin mallakar Faransa a matsayin ummul haba’isin dukkanin musibu a kan kasar Aljeriya, saboda haka malaman sun bukaci gwamnatin Aljeriya, da ta dakatar da duk wata hulda ta kasuwanci da tattalin arziki tare da kamfanonin kasar Faransa.
 

 

4004449

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha