IQNA

Qatar Ta Yi Lale Marhabin Da Tattaunawar Fahimtar Juna Da Ke Gudana Tsakanin Iran Da Saudiyya

18:19 - October 13, 2021
Lambar Labari: 3486422
Tehran (IQNA) gwamnatin Qatar ta yi lale marhabin da tattaunawa tsakanin Iran da Saudiyya, tare da jaddada cewa ba zata kulla alaka da Isra’ila ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Al-nashra ya bayar da rahoto cewa, ministan harkokin wajen kasar Qatar Muhammad Bin Abdulrahman Al Thani ya yi bayani a kan matsayin kasarsa dangane da batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a Afghanistan, da kuma batun kulla alaka da wasu kasashen larabawa suke yi da Isra’ila, da kuma batun alakar kasashen larabawa da Iran.
 
Ya ce dangane da batun kasar Afghanistan matsayin kasarsa a bayyane yake, kan cewa matukar ana son a taimaka ma al’ummar Afghanistan a halin yanzu dole ne sai an yi mu’amala da kungiyar Taliban wadda take rike da ragamar lamurran kasar.
 
A kan haka ya ce, kasarsa za ta ci gaba da yin aiki mai shiga tsakanin kasashe da kuma masu rike da ragamar harkokin mulkin Afghanistana halin yanzu, domin samun damar taimaka ma al’ummar kasar, wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa, da kuma saukaka musu yanayi na rayuwa.
 
Dangane da batun alakar kasashen larabawa da Iran kuwa, ministan harkokin wajen kasar Qatar ya ce, kasarsa tana da kyakkyawar alaka mai karfi tare da kasar Iran, wanda kuma hakan ya kamata ya kasance tsakanin Iran da sauran kasashen larabawa, kamar yadda ya kirayi sauran kasashen larabawa da su daina shiga cikin harkokin Iran na cikin gida, matukar dai suna son zaman lafiya
 
Sannan kuma ya ce ya yi farin ciki matuka dangane da gagarumin ci gaban da aka samu a tattaunawar da ke gudana yanzu haka tsakanin gwamnatocin Saudiyya da Iran, domin kara samun fahimtar juna, wanda kuma dama haka ya kamata ya kasance.
 
Dagane da hankoron kulla alaka da Isra’ila ada wasu gwamnatocin kasashen larabawa suke ta yi kuwa a halin yanzu, ministan harkokin wajen kasar Qatar ya bayyana cewa, kasarsa ba ta kulla alaka da Isra’ila ba, matukar dai ba a baiwa Falastinawa hakkokinsu ba, da hakan ya hada da kafa kasar Falastinu mai cin gashin kanta.
 

 

4004578

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha