IQNA

Sallar jam'i Ta Farko A Farfajiyar Hubbaren Hubbaren Imam Hussain (AS) A Karbala Bayan Janye Dokar Corona

20:59 - October 13, 2021
Lambar Labari: 3486423
Tehran (IQNA) bayan sanar da janye dokar hana taruka saboda kauce wa yaduwar cutar corona an gudanar da sallar jam'i ta farko farfajiyar hubbaren Imam Hussain (AS).

Bangaren yada labarai na hubbaren Karbala ya sanar da cewa, bayan sanar da janye dokar hana taruka saboda kaucewa yaduwar cutar corona an gudanar da sallar jam'i ta farko farfajiyar hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin na Karbala.

Mutane da dama ne suka halarci wannan sallar jam'i inda aka sallolin Azuhur da La'asar, duk kuwa da cewa har yanzu akwai ka'idoji da aka gindaya na kiwon lafiya, wanda ya zama wajibia  kiyaye su.

Sheikh Salah Karbala'i babban malami mai kula da harkokin hubbaren shi ne dai ya jagoranci limancin sallolin.

 

 

 

4004381

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hubbaren Imam Hussain ، farfajiya ، cutar corona ، kiwon lafiya ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha