IQNA

Tsohon Sakataren harkokin Wajen Amurka Colin Powell Ya Mutu Bayan Kamuwa Da Corona

19:17 - October 18, 2021
Lambar Labari: 3486441
Tehran (IQNA) Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell ya mutu yana da shekaru 84, sakamakon kamuwa da cutar Corona.

Colin Powell, fitaccen dan jam’iyyar Republican kuma bakar fata na farko da ya fara aiki a matsayin Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya mutu a inda yake karbar magani a cibiyar kula da harkokin kiwon lafiya ta kasa Walter Reed, kamar yadda iyalansa suka sanar.

Haka nan kuma Iyalinsa sun gode wa ma'aikatan kiwon lafiya "saboda kulawar da suka nuna." An bayyana dalilin mutuwar da cewa sakama ne na kamuwa da corona mai tsanani, inda ya rasua  safiyar yau Litinin.

Powell tsohon Janar ne na soja, wanda ya yi shekaru 35 yana aiki, wanda ya kai ga samun tauraruwa hudu kafin daga bisani kuma ya shiga siyasa.

Ya yi aiki a matsayin shugaban Hafsoshin sojin Amurka, wanda shi ne matsayi mafi girma na soja a Ma'aikatar Tsaro ta Amurka, a lokacin Shugabancin George H.W. Bush, kuma shi ne ɗan Afirka na farko da ya riƙe wannan matsayin.

Bayan nan kuma tsohon shugaban kasar ta Amurka George W. Bush ya ba shi matsayin sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka, wanda shi ma a lokacin shi ne bakar fata dan asalin Afirka da ya fara rike wannan mukami a kasar Amurka.

 

 

4006200

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha