Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da wani babban taron Maulidin manzon Allah (SAW) a birnin Lahur na kasar Pakistan tare da halartar dubban mutane, da suka hada da malamai da kuma manyan jami'an gwamnati.
A bisa gayyatar Kungiyar Minhaj Al-Quran ta Duniya, Ja’far Ronas; shugaban karamin ofishin jakadancin jumhuriyar musulunci ta Iran a Lahore, da kuma shugaban ofishin kula da harkokin al'adu na kasar Iran a Pakistan, su ma sun halarci wannan taro a madadin kasar.
Malaman addinin Musulunci daban -daban, a yayin halartar wannan taro na haɗin kai dangane da zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW), sun jaddada muhimmancin haɗin kan al'ummar musulmi.
A wurin wannan babban taro, Allamah Taher Al-Qaderi; Shugaban kungiyar kasa da kasa ta Minhaj Al-Quran daga Canada ya gabatar da jawabi ta yanar gizo kai tsaye ga mahalarta taron.
4006803