IQNA

Taron Maulidin Manzon Allah (SAW) A Kudancin Beirut Lebanon

21:50 - October 23, 2021
Lambar Labari: 3486465
Tehran (IQNA) an gudanar da zaman taron Maulidin Manzon Allah (SAW) a birnin Beirut na Lebanon.
Shafin Al'ahad ya bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta gudanar da gagarumin biki a daren jiya a yankin Al-Jamous na gundumar Dahiya, kudancin Beirut, a bukukuwan maulidin manzon Allah  (SAW) da kuma makon hadin kan Musulunci.
 
An fara bikin tare da karanta ayoyi daga littafin Allah, da kuma yin wakokin addini da jawabin Sayyid Hassan Nasrallah da kuma wasu malamai.
 
A wani bangare na jawabinsa, babban sakataren kungiyar Hizbullah a Lebanon ya bayyana muhimmiyar nasarar da Manzon Allah (SAW) ya samu a matsayin samar da babban sauyi na imani ga bil'adama tare da wannan addinin ya zama manufa ta har abada.
 
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4007254
Abubuwan Da Ya Shafa: kungiyar Hizbullah ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha