IQNA

An Kawo Karshen Taron Makon Hadin Kan Musulmi Karo Na Talatin Da Biyar

14:25 - October 24, 2021
Lambar Labari: 3486467
Tehran (IQNA) Taron makon hadin kan musulmi karo na 35 a birnin Tehran ya kawo karshe.

An kammala taron hadin kan musulmi karo na 35 a birnin Tehran, inda fitattun malamai, masana daga sassa daban-daban na duniya suka yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan da suka shafi duniyar Musulmi.
Sanarwar bayan taron da aka fiyar jiya Asabar wajen rufe taron ta bayyana halin da duniya ke ciki a yanzu da kuma kokarin ganin bayan wuce gona da iri na wasu kasashen duniya domin samar da zaman lafiya a fadin duniya."
 
Cimma wannan buri na bukatar hadin kan kasa da kasa na gaskiya, nesa ba kusa ba daga duk wani matsin lamba ko barazana, da kuma kawo karshen tsoma bakin wasu kasashe.
 
A cewar sanarwar rufe taron‘’Rikici, yaki da tashe-tashen hankula da ta'addanci a duniya, musamman a kasashen musulmi, yana nuna bukatar kasashen musulmi su dauki matakan gaggawa domin warware wadannan matsaloli ."
 

4007496

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha