IQNA

Jagoran Juyin Musulunci A Iran:

Babban Abin Da Yake Hada Kan Dukkanin Musulmi Baki Daya Shi Ne Falastinu

18:36 - October 24, 2021
Lambar Labari: 3486470
Tehran (IQNA) a yayin ganawa da jami'an gwamnati da bakin da ke halartar Babban Taron Hadin Kan Musulmai na Duniya, Ayatullah Khamenei ya bayyana batun Falastinu a matsayin abin da ke hada kan musulmi.

Shafin yada labarai na ofishin Jagora ya bayyana cewa, a ci gaba da tarukan maulidin mai albarka na Annabi Mohammad Mustafa (A.S) da Imam Jaafar Sadegh (AS), a yau Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin wani ga jami'ai da bakin da ke halartar Taron kasa da kasa kan Hadin kan Musulmi, ya yi kira kan muhimman abubuwa guda biyu ga al'ummar musulmi, na daya inganta ci gaban Musulmi a dukkan fannonin rayuwar dan adam, na biyu kuma karfafa hadin kan Musulmi.

Inda ya jaddad cewa,  Hadin kan Musulmi wajibi ne daga abubuwan da suka zo cikin Alkur'ani, kuma tabbatar da babban burin samar da wannan hadin kai da dunkulalliyar al'umma guda daya ta musulmi na bukatar samar da fahimtar juna da yin riko da asasi na asalia  cikin addini, wanda dukkanin musulmi Shi'a da Sunna suka yi imani da shi, wato tauhidi da imani da manzon Allah da riko da kur'ani mai tsarki.

Ya ce wadannan abubuwan su ne suka hada musulmi, kuma su ne asasi na musulunci, duk wanda ya yarda da su to musulmi ne kuma yana cikin addini musulunci, sabanin fahimta kuma kan wasu abubuwa kuwa, ba shi ne asasi ba.

A yayin da yake taya al'ummar Iran da dukkanin al'ummar musulmi na duniya murnar zagayowar lokacin haihuwar manzon Allah (SAW) kuwa, Ayatullah Khamenei ya kira haihuwar manzon Allah a matsayin babban lamari kuma farkon sabuwar rayuwa a cikin falalar Ubangiji ga rayuwar dan adam.

 

4007580

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha