IQNA

An Kira Da A Gudanar Da Sallar Rokon Ruwa A Fadin Kasar Saudiyya

19:03 - November 02, 2021
Lambar Labari: 3486504
Tehran (IQNA) Sarkin Saudiyya ya gayyaci jama'a daga sassa daban-daban na kasar domin gabatar da sallar rokon ruwan sama a ranar Alhamis.​

Tashar russia Today ta bayar da rahoton cewa, Sarkin Saudiyya ya fitar da wata sanarwa inda ya bukaci a gudanar da Sallar rokon  ruwan sama a fadin kasar sakamkon karancin ruwan sama da aka samu a kasar.

Ofishin masarautar Saudiyya ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: "Bisa ga abin da aka samu a cikin sunnar Manzon Allah (S.A.W) wajen gabatar da sallar rokon  ruwan sama, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud ya gayyaci jama'a a kasar da a gudanar da sallar rokon  ruwan sama a ranar Alhamis 4 ga watan Nuwamba a duk fadin kasar Saudiyya. 

Bayanin ya ce: Lallai kowa ya tuba ya nemi gafara da komawa ga Allah madaukaki, da kyautata wa bayinsa, da yawaita nafila kamar zakka da salla da zikiri, da saukaka aiki ga bayin Allah da kawar musu da bakin ciki, watakila Allah ya cece mu, ya ba mu abin da muke so.  

A karshen wannan bayani yana cewa: Ya dace duk wanda ya samu iko  ya yi wannan sallar domin aiki da Sunnar Manzon Allah (SAW) ce wajen  bayyana bukata ga Allah Madaukakin Sarki, da dagewa a kan addu'a, domin Allah yana son bayinsa masu dagewa da addu'a.

 

4009975

 

captcha