IQNA

Karatun Kur'ani Tare Da Makaranta Daga Masar Da Iran A Birnin Lahore Na Pakistan

19:57 - November 06, 2021
Lambar Labari: 3486520
Tehran (IQNA) Bisa gayyatar da makarantar hauza ta Orwa al-Wathqi ta yi a birnin Lahore, mahardatan Iran da na Masar sun halarci taron kur'ani da aka gudanar a cibiyar tare da karanta ayoyin kur'ani.

A bisa rahoton iqna daga Pakistan, an gudanar da bikin ne a ranar 4 ga watan Nuwamba, tare da halartar Karim Mansouri, makaranci na kasa da kasa daga Iran, da Sheikh Mahmoud Kamal al-Najjar da Suleiman al-Shahab, wasu matasan Makaranta kur'ani daga Masar.
 
An gudanar da karatun ne a Masallacin Atiq da ke Lahore, wanda jami'ai da kuma 'yan makarantar hauza ta Orwa al-Wathqi da kuma malamai suka halarci wurin.
 
Sayyid Ziaullah Shah Bukhari, fitaccen malamin Sunnah kuma shugaban kungiyar Hadith ta kasar Pakistan, a lokacin da yake maraba da masu karatu da suka halarci taron, ya jaddada wajibcin kara mai da hankali kan lamurra da suka kur'ani mai tsarki a cikin harkokin musulmi.
 
An gabatar da wannan shiri ne bayan Sallar Magariba da Isha'i, sannan Karim Mansouri ya karanta addu'ar kammalawa. 
 
https://iqna.ir/fa/news/4010785
Abubuwan Da Ya Shafa: mai da hankali Karim Mansouri
captcha