IQNA

Azhar Ta Kirayi Al’ummar Iraki Da Su Hada Kai Domin Fuskantar Makircin Makiya

15:55 - November 08, 2021
Lambar Labari: 3486528
Tehran (IQNA) Cibiyar Azhar ta yi Allah wadai da yunkurin kashe firaministan kasar Iraki tare da yin kira ga al'ummar Iraki da su tsaya tsayin daka su kiyaye hadin kan su.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mawazin News cewa, Al-Azhar ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da yunkurin kisan gillar da aka yi wa firaministan kasar Iraki Mustafa al-Kadhimi, inda ta jaddada cikakken hadin kai ga kasar Iraki da kuma goyon bayanta kan abin da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasar.
 
A cikin wannan bayani, Al-Azhar ta yi kira ga al'ummar Iraki da su hada kansu, su ciyar da kasarsu gaba,  da tsayin daka wajen yakar makiyanta, da kuma hana masu mummunan nufi, da ba sa son alheri ga kasar cimma wannan manufa tasu a kan Iraki.
 
Al-Azhar ta roki Allah Ta'ala da ya kare kasar Iraki daga dukkan wani sharri, ya azurta ta da tsaro da kwanciyar hankali da wadata.
 
Jami'an tsaron Irakin sun sanar da kai hari kan gidan firaministan Iraki da jirage marasa matuka, sannan daga bisani  jama'a da kungiyoyi da jami'an kasashen waje sun yi Allah wadai da harin.
 
A halin da ake ciki kuma, kungiyoyin da ke da kusanci da masu zanga-zangar adawa da sakamakon zabe sun jaddada bukatar kafa kwamitin kwararru domin tantance bayanai da aka samu kan lamarin da kuma abubuwan da ke tattare da hakan.
 

4011383

 

 

 

 

 

captcha