IQNA

Mutumin Da Ya Kai Harin Masallacin Christchurch Zai Daukaka Kara Kan Hukuncin Da Aka Yanke Masa

21:40 - November 08, 2021
Lambar Labari: 3486530
Tehran (IQNA) mutumin da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai saboda kisan gillar da ya yi wa wasu masallata 51 a New Zealand na da niyyar daukaka kara kan hukuncin.

Tashar France 24 ta bayar da rahoton cewa, Brenton Tarrant, dan kasar Australia mai akidar kin jinin musulmi wanda ya kai hari a kan masallata tare kashe 51 daga cikinsu a garin Christchurch na  New Zealand, a watan Maris din shekarar 2019, inda ya kai hari kan masallatai biyu na Al Nour da Linwood, yana shirin daukaka kara kan hukuncin da wata kotu ta yanke a kansa na daurin rai da rai.

Brenton Tarrant wanda ya watsa hotunan bidiyo na tsawon mintuna 17 a shafin facebook da ke nuna abin da ya aikata na kisan musulmi a masallaci, har yanzu bai yi nadama kan wannan mummunan aiki da ya tafka ba.
 
TarrantTrent dai ya kalubalanci hukuncin kotun ne bisa hujjar cewa ya riga ya amsa laifin kashe musulmi 51 tare da raunata wasu 40 na daban, ya kuma yi zargin cewa an ci zarafinsa a lokacin tambayoyi da kuma tsare shi a gidan yari.
 
An yanke wa wannan dan ta’adda hukuncin daurin rai da rai ne ba tare da hakkin yafewa ba. Wannan shi ne karon farko da aka yanke wa wani mai laifi irin wannan hukunci a kasar New Zealand.
 
Christchurch shi ne birni mafi girma a kudancin New Zealand kuma tsakiyar yankin Canterbury. Haka nan kuma shi ne birni na uku mafi yawan jama'a a New Zealand bayan Auckland da Wellington, inda mutane kimanin 404,000 suke rayuwa a cikinsa.
 
Kisan da wannan dan ta'adda ya yi a kan musulmi a birnin Christchurch, ba a taɓa yin irinsa ba a tarihin New Zealand, wanda kuma wannan laifin yasa an samar da  sauye-sauye a cikin dokokin tsaro da ta'ammuli da makamai a kasar.
 
 
 

4011619

 

 

 

captcha