
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Kotun kolin Amurka na nazarin kara a kan ‘yan sandan tarayya bisa zargin yin leken asiri a wani masallaci na musulmi.
Mutane 3 ne da suka hada da limamin masallacin Orange County da ke Los Angeles jihar California, suka kai karar hukumar ‘yan sandan Amurka bisa zargin laifin leken asiri kan masallacin, wanda kuma a jiya Litinin kotun ta fara bin kadun batun.
Musulmin sun ce tun a shekara ta 2001 hukumar FBI ke yi musu leken asiri kwakwaf, ba don sun aikata wani laifi ba, sai domin kawai su musulmi ne, wanda hakan ya yi hannun riga da dokokin Amurka.
Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta yi iƙirarin cewa ayyukan leƙen asirin 'yan sanda ba su da wata alaƙa da wani addini, 'yan sanda na da hakkin su yi aikinsu a kan kowa kuma a kowane wuri.
Tun bayan harin 11 ga watan Satumba, Musulmai sun zama abin nuna wa wariya da zargi a cikin Amurka, duk kuwa da cewa musulmi suna nisanta kansu da 'yan takfir masu da'awar jihadi wadanda babu wanda ya tsira daga ayyukan ta'addancinsu, bil hasali ma a mafi yawan lokuta musulmi ne suka fi kai wa hare-hare da sunan jihadi.
Shekaru bakwai da suka gabata, Craig Montiel, wanda ake yi wa lakabi da “Farooq al-Aziz,” ya bayyana cewa: “Hukumar AFBI ta biya ni kudi domin na kutsa cikin masallatan Los Angeles da Orange County a Kudancin California, domin yin leken asiri a kan musulmi.