
Taron wanda babban bankin kasar Saudiyya ya dauki bakuncinsa gudanar da shi a birnin Jeddah, an tattauna batun fasahar samar da kudade ta FinTech da kayan aikin raya kasuwar hada-hadar kudi ta Musulunci.
Taron dai an yi shi ne mai taken "Fasahar Harkokin Kudade na Musulunci" wanda ya mayar da hankali kan ci gaban Kasuwa da Ingantacciyar hanyar bunkasa ta, wanda Dr. Mohammad Azami Omar daga Malaysia, Manajan Daraktan Cibiyar Horarwa kan fasahar harkokin Kudade ta Musulunci ta kasa da kasa ya jagoranta.
Dr. Mohammad Azami ya ce: "An kiyasta yawan hada-hadar da ke da alaka da kudaden Musulunci a shekarar 2020 zuwa dala biliyan 400, wanda ke nufin fasahar hadahadar kudi tana da kaso mai yawa a kasuwannin duniya.
Ana hasashen shirin FinTech zai bunkasa kuma zai samu kudade da za su dala biliyan 100 nan da 2025, akan haka, Islamic Fintech za ta samu kaso mai tsoka a kasuwa.
Taron ya samu halartar wakilai daga kasashen Saudiyya, Indonesia, Malaysia da wasu kasashe da dama.