IQNA

Ra’isi: Iran Da Turkiya Na Taka Muhimmiyar Rawa Domin Karfafa Zaman Lafiya A Yankin

18:24 - November 15, 2021
Lambar Labari: 3486560
Tehran (IQNA) Raisi ya tabbatar da cewa, dangantakar kut da kut tsakanin Iran da Turkiyya ta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin

Shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya tabbatar da cewa, dangantakar kut da kut tsakanin Iran da Turkiyya ta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, inda ya yaba da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna.

A yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu a yau Litinin, shugaban kasar Iran ya bayyana cewa, raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, musamman a fannin ciniki da tattalin arziki, na da moriya mai yawa ga kasashen biyu, kamar yadda kuma hadin gwiwa a tsakaninsu yana cikin ajandar kasashen biyu.

Raisi ya yi la'akari da dangantakar kut-da-kut da ke tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, inda ya ce: Ya kamata a sauya hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu zuwa hadin gwiwa a matakin kasa da kasa, kuma irin wannan mu'amala za ta yi tasiri a cikin siyasar kasa da kasa da kawo daidaito a duniya, idan aka yi la'akari da muhimmin matsayin kasashen biyu.

Ministan harkokin wajen kasar Iran a nasa bangaren  ya sanar da cewa an cimma yarjejeniyar  tsara taswirar ayyukan hadin gwiwa na dogon lokaci tsakanin Iran da Turkiyya, tare da bayyana fatan ganin an sanya hannu kan takardar yarjejeniyar a ziyarar da shugaban kasar Turkiyya zai kai kasar Iran.

Ministan harkokin wajen Husein Amir Abdullahyan ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da takwaransa na a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Tehran, inda ya ce, mun amince da yarjejeniyar aiki tare na dogon lokaci a tsakanin Tehran da Ankara, kuma muna fatan a nan gaba kadan shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan  zai kai ziyara Tehran, inda za a rattaba hannu kan wannan yarjejeniya.

Ya kara da cewa: Mun amince da fara tattaunawar diflomasiyya a wannan fanni kuma muna fatan zai taimaka matuka wajen cimma manufofin da kasashen biyu suka sanya a gaba na bunkasa ci gabansu a bangarori daban-daban domin amfanin al’ummominsu.

A yayin da yake ishara da rikicin kasar Yemen, ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana fatansa na ganin an kawo karshen yakin basasar da ake yi a kasar ta Yemen ba tare da wani bata lokaci ba, tare da janye takunkumai da kuma killace kasar ta Yemen, da kuma isar da kayayyakin jin kai ga al’ummar wannan kasa ta musulmi cikin gaggawa.

Dangane da abubuwan da ke faruwa a Labanon kuwa, ya kara da cewa: Muna bibiyar abubuwan da ke faruwa a kasar ta Labanon, kuma mun damu matuka kan halin da ake yunkurin jefa wannan kasa a ciki, musamman ma yadda wasu kasashen larabawa suka dauki matakan rufe ofisoshinsu an diflomasiyya a Lebanon da kuma korar jakadun Lebanon daga kasarsu kan abin da bai ya kai ya kawo ba.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya tabbatar da cewa kasarsa ta kuduri aniyar karfafa hadin gwiwa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen yaki da ta'addanci da samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin.

Cavusoglu ya jaddada cewa, kasarsa na kokarin kara habaka dangantakar da ke tsakaninta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda ya ce: Turkiyya na daukar sabuwar gwamnatin Iran a matsayin gwamnatin da ke neman cimma sakamako mai kyau, kuma ta kuduri aniyar kara hadin gwiwa da Tehran.

 

4013505

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha