IQNA

Babbar Jam'iyyar Adawa A Uganda Ta Yi Gargadi Kan A Daina Jingina Harin Ta'addanci Ga Musulmi

18:36 - November 23, 2021
Lambar Labari: 3486596
Tehran (IQNA) Kakakin wata jam'iyyar Uganda ya yi gargadi game da jingina wa musulmi alhakin hare-haren ta'addanci da aka kai a kasar, yana mai cewa al'ummar Musulman Uganda na cikin firgici kan zarginsu da hannu a hare-haren ta'addancin na baya-bayan nan.

Kakakin jam'iyyar FDC a kasar Uganda Ibrahim Ssemujju Nganda, ya shaidawa taron manema labarai cewa al'ummar musulmin kasar Uganda na cikin firgita dangane da zargin hannu a hare-haren ta'addanci na baya-bayan nan.
 
Nganda ya ce, ana ayyana masallatai a matsayin cibiyoyi masu tsattsauran ra'ayi kuma akwai fargabar cewa jami'an tsaro za su fara kai hari a wuraren ibada na musulmi.
 
Da yake sukar kalaman shugaban na Uganda na baya-bayan nan, ya ce: “Yuri Mosivini ya zama mai fassara addinin Musulunci, Yana daukar kansa kwararre wanda ya san koyarwar addinin musulunci, to dole ne ya dakatar da wadannan maganganun.
 
A cikin jawabinsa na karshen mako Mousavini ya ce wadanda ke da hannu a ayyukan ta'addanci suna da sunayen musulmi ne, yana mai kokarin danganta harin ta'addancin ga musulmi.
 
Nganda ya ce "Hari kan masallatai, kama mutanen da ke zuwa makarantun addini wani nau'i ne na wariya." Wajibi ne hukumomin tsaro su yi taka-tsan-tsan wajen tunkarar wannan matsala.
 
A ranar Talatar makon da ya gabata ne dai wasu bama-bamai uku suka fashe a birnin Kampala babban birnin Uganda, inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu da dama, wanda kuma an kai harin ne a gaban ginin majalisar dokokin Uganda da kuma hedikwatar 'yan sanda.
 
Rundunar ‘yan sandan Uganda ta tabbatar da cewa an kashe ‘yan ta'addar da suka kai hare-haren.

 

4015674

 

 

 

captcha