IQNA

22:56 - November 24, 2021
Lambar Labari: 3486602
Tehran (IQNA) sabon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar kan Yemen ya ce yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan al'ummar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 377 cikin shekaru 7.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, sama da kashi 60 cikin dari na wadanda suka mutu, sun rasu ne sakamakon matsalolin da yakin ya jefa su a  ciki ne, da hakan ya hada da rashin abinci da rashin ruwan sha, da rashin magunguna, da kuma rusa asibitoci da sauran abubuwa wadanda suka haddasa matsaloli masu yawa ga al'ummar kasar.

Sannan kuma a cewar rahoton kimanin kashi 40 cikin dari sun rasu ne sakamakon kaddamar da hare-hare da jiragen yaki da kuma musayar wuta tsakanin bangarorin da suke fafatawa.

Rahoton ya ce, a halin yanzu fiye da kashi 65 cikin dari na mutanen Yemen suna cikin mawuyacin hali da bukatar taimakon gaggawa na abinci da abiin sha da magunguna, sakamakon wannan yaki na Saudiyya a kan kasarsu.

Tun a cikin shekara ta 2015 ne dai gwamnatin masarauatr Al Saud ta fara kaddamar da hare-hare kan al'ummar kasar Yemen, da sunan yunkurin dawo da Hadi Rabbuhu Mansur kan mulkin kasar, bayan da ya yi murabus kuma ya tsere zuwa birnin Riyad, lamarin da bai tabbata ba har zuwa inda yau take, duk da  kashe dubban daruruwa na mutanen kasar, da kuma kashe daruruwan biliyoyin daloli da Saudiyya ta yi a wanan yaki.

4016083

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: