IQNA

'Yan Ta'addan ISWAP Sun Kashe sojojin Najeriya 7 A Kusa Da Iyaka Da Kamaru

17:02 - December 04, 2021
Lambar Labari: 3486641
Tehran (IQNA) A jiya ne dai wani hari da mayakan ISIL suka kai kan sojojin Najeriya ya kashe bakwai daga cikin sojojin a arewa maso gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Majiyoyin sojin Najeriya sun tabbatar da cewa an kashe sojojin Najeriya bakwai a ranar jiya Juma'a a wani harin ta'addanci da aka kai a sansanin sojojin da ke arewa maso gabashin Najeriya kusa da kan iyaka da kasar Kamaru.
 
Wasu gungun 'yan ta'addan da aka fi sani da Da'esh (ISWAP) sun kai hari a sansanin sojojin Najeriya da ke birnin Ran a ranar 3 ga watan Disamba, kuma an gwabza kazamin fada tsakanin su da sojojin Najeriya.
 
Rahoton na kamfanin dillancin labaran AFP ya ce maharan na tafiya ne a cikin wasu manyan motoci dauke da makamai masu sarrafa kansu, kuma sojojin Najeriya sun dakile harin, amma duk da haka sun rasa 7 daga cikin abokan aikinsu.
 
Ko a ranar 17 ga watan Satumba, kungiyar ta'addanci ta ISIS ta kashe sojojin Najeriya akalla 16 a kan hanyar Maiduguri zuwa Mongono a yankin tafkin Chadi.
 
Bayan mako guda da faruwar hakan, an kuma kashe sojojin Najeriya takwas a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a kusa da garin Dikova a yankin.
 

 

 

 

 

 
 
captcha