IQNA

Kuwait Ta Hana Wani Jirgin Ruwa Da Ke Dauke Da Kayan Isra'ila Tsayawa A Gabar Ruwanta

14:42 - December 05, 2021
1
Lambar Labari: 3486644
Tehran (IQNA) Gwamnatin Kuwait ta haramtawa jiragen ruwa da ke dauke da kayayyakin Isra'ila shiga tashoshin jiragen ruwanta.
Gwamnatin Kuwait ta sanar da cewa, za ta haramta wa jiragen ruwa na kasuwanci da ke dauke da kayayyakin Isra'ila shiga tashoshin jiragen ruwanta da kuma safarar jiragen ruwa zuwa Isra'ila.
 
Ministan harkokin jama'a na Kuwait kuma ministan sadarwa da fasaha Rana Al-Fars ya sanar da fitar da wata doka ta haramtawa jiragen ruwa 'yan kasuwa da ke dauke da kayayyaki shiga cikin yankunan Kuwait, kamar yadda kuma ta haramta jiragen da ke tashi daga gabar ruwanta zuwa Isra'ila.
 
Wannan hukuncin na Kuwait ya yi daidai da matakin da kasashen Larabawa suka dauka na kakabawa Isra'ila takunkumi a cikin kungiyar kasashen Larabawa a shekarun 1950. 
 
Kuwait na daya daga cikin kasashen larabawa da ke sakawa gwamnatin yahudawan Isra'ila takunkumi, kasashe  15 daga cikin mambobi 22 na kungiyar kasashen Larabawa ciki har da Kuwait ba su amince da gwamnatin sahyoniyawa ba.
 
 

4018481

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
ABDURASHID HARUNA
0
0
Nima ina goyan bayan wannan matakin da kasar kuwait ta dauka akan tsinanniyar haramtacciyar kasar israila
captcha