IQNA

An Yi Canje-Canje A Manhajar Karatu A Wasu Kasashen Larabawa Domin Kare Isra'ila

22:08 - December 12, 2021
Lambar Labari: 3486675
Tehran (IQNA) Wata kungiyar Isra'ila ta ba da rahoton cewa an samu sauyi a manhajar karatu a wasu kasashen Larabawa domin kawar da sukar Yahudawa da gwamnatin Isra'ila a cikin litattafansu.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Cikakkun bayanai da kungiyar Anti-Defamation Union (ADL) ta rubuta, wadda a cewar shafinta na yanar gizo, tana gudanar da ayyukan tallafa wa gwamnatin sahyoniyawan a matsayin kasa ta yahudawa dimokuradiyya da kuma sanya ido kan kamfen na kyamar sahyoniyawa a fadin duniya.

Kungiyar ta ce bisa binciken da ta gudanar ta gano cewa, an samu sauyi a manhajar karatu a wasu kasashen Larabawa domin kawar da sukar Yahudawa da gwamnatin Isra'ila a cikin litattafansu da ake koyar da yara.

Bayanin ya ce: "Sake fasalin ilimi a Gabas ta Tsakiya yana daga cikin ci gaba da aka samu  wajen yaƙi da tsattsauran ra'ayi," in ji ƙungiyar ta yahudawa, tana mai ba da misali da wani rahoto na baya-bayan nan tare da haɗin gwiwar Cibiyar Canji ta Duniya ta Tony Blair.

Kungiyar dai tana karkashin tsohon Firaministan na Burtaniya ne, kuma mai ba da shawara ta musamman kan harkokin kasa da kasa a kungiyar yaki da kyamar yahudawa.

An hada rahoton ne a cikin shafuka 45 mai taken "Koyar da Zaman Lafiya da Juriya a Duniyar Larabawa Shekaru Biyu Bayan 9/11."

 

4020185

 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: yahudawa ، bisa bincike ، ayyuka ، tallafa wa ، dimokuradiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha