IQNA

Tehran (IQNA) Sheikh Abdulfattah Taruti shahararren makarancin kur'ani Masar ya bayar da bayanin cewa, an samu gawar marigayi Sheikh Muhammad Al-laithi ba ta yi komai ba, bayan shekaru 5 da rasuwarsa.

Sheikh Abdulfattah Taruti  ya ce, bayan shekaru biyar da rasuwar Fitaccen Makarancin Kur'ani Sheikh Muhammad Al-laithi , mahaifinsa ya rasu, inda bisa ga al'ada a kasar masar a kan bizne iyalan gida guda kabrukansu kusa da juna.

A lokacin gina kabarin mahaifinsa  a kusa da kabarinsa, mai aikin ginar kabarin ya tono kabarin Sheikh Muhammad Al-laithi da ke gefe, kuma an ga gawarsa kamar yadda aka bizne shi da gangar jikinsa ba ta yi komai ba, bayan shekaru biyar da rasuwarsa.

Abubuwan Da Ya Shafa: Sheikh Muhammad Al-laithi ، bayan shekaru biyar ، marigayi ، ،