IQNA

Msallacin Tarihi Na Kafr Sheikh A Masar Na Fuskantar Hadarin Rushewa

21:40 - December 21, 2021
Lambar Labari: 3486713
Tehran (IQNA) Masallaci daya tilo mai dadadden tarihi a birnin Bila da ke lardin Kafr al-Sheikh na kasar Masar yana kan hanyar rugujewa.

Jaridar Albalad ta bayar da rahoton cewa, masallacin Abu Ghnam, wanda shi ne tsohon masallacin daya tilo a birnin Bila a cikin lardin Kafr Sheikh, an bukaci sake gyara shi tun shekara ta 2000, amma kawo yanzu babu wani mataki da aka dauka.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, ruwan ya rika sauka a kan masallata, lamarin da ya sa masallatan suka yi gaggawar ficewa daga masallacin.
 
Sama da shekaru 20 mazauna garin na Bila na korafin rashin kyawun masallacin da rugujewar katangarsa, amma hukumomi sun ba su mayar da hankali kan batun ba, wanda hakan yasa a halin yanzu masallacin na cikin hatsarin rugujewa a kowane lokaci.
 
An gina wannan Masallacin dai tun fiye da shekaru 742 da suka gabata, kuma ba a sake gina shi ba tun bayan sake gina shi a zamanin mulkin Ismail Pasha.
 
Wannan masallacin da ake kallonsa a matsayin babban wurin tarihi mai kima, a yanzu yana cikin yanayi mai hatsari.
 
 

4022621

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha