IQNA

An Gudanar Da Janazar jakadan Iran A Kasar Yemen

19:00 - December 23, 2021
Lambar Labari: 3486718
Tehran (IQNA) an gudanar da jana’izar jakadan kasar Iran a Yemen bayan rasuwarsa a ranar Talata saboda kamuwa da cutar corona.

Ayatollah Muhammad Hassan Akhtari sakataren cibiyar Ahlul bait ta duniya ya isar da sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar jakadan na Iran tare da bayyana shi a matsayin mutum mumini.
 
A safiyar jiya Laraba ce aka gudanar da jana’izar jakadan kasar Iran a Yemen bayan rasuwarsa a ranar Talata saboda cutar Covid 19.
 
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa Hassan Irlou ya kamu da cutar Covid-9 ne a birnin San’a, babban birnin kasar Yemen amma saboda rashin bada hadin kai na wasu kasashen yankin ya sa cutar ta wahalar da shi.
 
Bayan isowa da shi birnin Tehran likitoci sun yi kokarin ceton rayuwarsa daga cutar, sun yi dukkan abin da zasu iya amma a safiyar Talata aka bada sanarwar rasuwarsa.
 
Hassan Irlou kwararren jami’in diflomasiyya ne a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran. Ya rike mukamai da dama a ma’aikatar kafin ya zama jakadan Iran a kasar Yemen, daga ciki ya taba zama mataimkin ministan harkokin wajen kasar a harkokin kasar Yemen. An nada shi shi jakadan Iran a Yemen a shekara ta 2020.
 
A lokacin ne kuma Amurka ta dora masa takunkumi, inda ita ma Iran ta maida martani, inda ta dorawa jakadan Amurka a Yemen Christopher Hansel takunkumi
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4022812.
captcha