IQNA

Wasu Lauyoyi A Indiya Sun Yi Zanga-Zangar Neman A Dauki Mataki Kan 'Yan Hindos Masu Tsattsauran Ra'ayi

22:37 - December 28, 2021
Lambar Labari: 3486744
Tehran (IQNA) wasu lauyoyi a kasar India sun gudanar da jerin gwano domin yin kira ga gwamnati ta dauki mataki a kan 'yan addinin Hindus masu tsattsauran ra'ayi.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a yau wasu lauyoyi a kasar India sun gudanar da jerin gwano domin yin kira ga gwamnati ta dauki mataki a kan 'yan addinin Hindus masu tsattsauran ra'ayi, wadanda su ne da hannu wajen kisan musulmi a kasar.

Rahoton y ace, a cikin wata wasika da suka aike wa alkalin alkalan Indiya, lauyoyin sun bukaci a dauki mataki  kan mabiya addinin Hindu masu tsattsauran ra'ayi saboda tada tarzoma da nuna kyama ga musulmi.

Masu tsattsauran ra'ayin addinin Hindu sun yi kira da a yi wa Musulman Indiya kisan kiyashi a wasu taruka biyu da suka gudanar a babban birnin kasar New Delhi da kuma Uttarakhand a cikin wannan watan Disamba.

Lauyoyin sun bayyana a cikin wasikar tasu cewa: "Wadannan taruka da ayyukan da aka yi a cikin su wata gayyata ce a fili zuwa ga kisan musulmi, da kuma babbar barazana ga hadin kan al’ummar kasar, da kuma zubar da mutuncinta a idon duniya."

Wasikar ta zo ne bayan da ‘yan jam’iyyun adawa suka nuna rashin amincewarsu da shirun da Firai Ministan Indiya Narendra Modi ya yi kan kiran da ‘yan Hindu masu tsatsauran ra’ayi suka yi na kawar da musulmi a kasar ta India.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne ‘yan sandan Indiya suka sanar da fara gudanar da bincike kan kiraye-kirayen kisan kiyashin da masu tsattsauran ra’ayin addinin Hindu suka yi a kan musulmi a wani gangami a yankin Haridwar da ke Uttarakhand da suka yi.

Ana dai zargin jam'iyya mai mulki karkashin jagorancin Narendra Modi da ingiza masu tsattsauran ra’ayin addinin Hindu domin  muzgunawa musulmi da sauran tsiraru a kasar tun bayan da ta hau mulki a shekara ta 2014, duk da cewa jam'iyyar ta musanta  cewa tana da hannu a cikin lamarin.

 

4024365

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: addinin hindu
captcha