IQNA

An Yi Allawadai Da Kai Farmaki Kan Cibiyar Musulmi da Ke Jihar Arizona A Amurka

19:38 - December 29, 2021
Lambar Labari: 3486747
Tehran (IQNA) Majalisar musulmin Amurka ta yi Allah wadai da harin da wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka kai a wata cibiyar addinin musulunci a garin Tucson na jihar Arizona a farkon makon nan.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Majalisar musulmin Amurka a cikin wata sanarwa da ta fitar ta yi Allah wadai da matakin, inda ta jaddada bukatar tallafawa daidaikun mutane wajen gudanar da ayyukansu na addini da kuma tabbatar da tsaron masallatai.

A cewar faifan bidiyon da aka fitar, mutane uku (mata biyu da namiji daya) sun yi jifa da duwatsu a kofofi da tagogin Cibiyar Musulunci ta Tucsan inda suka far wa mutum daya a lokacin da ya yi kokarin hana su.

Soheil, memba a majalisar gudanarwa na Cibiyar Musulunci ta Tucson, ya ce lamarin bai dace ba kuma ba a taba ganin irinsa ba.

A cikin 'yan watannin nan, birane da jihohi da dama a Amurka sun fuskanci hare-hare kan cibiyoyin addinin Musulunci.

A tsakiyar watan Disamba ne Majalisar Dokokin Amurka ta zartar da wata doka da ta kafa wani ofishi na musamman a ma'aikatar harkokin wajen Amurka don yaki da kyamar Musulunci a duniya.

Duk da cewa Musulman Amurka sun bayyana amincewa da dokar a matsayin wata nasara mai cike da tarihi ga musulmi, har yanzu Washington ba ta iya magance kalubalen kyamar Musulunci da hare-haren da ake kai wa musulmi a kasar ba.

 

4024386

 

 

captcha