IQNA

Masallatai Da Majami'oi Sun Taimaka Wajen Gudanar Rigafin Corona A Kenya

21:30 - January 02, 2022
Lambar Labari: 3486771
Tehran (IQNA) Amincewa da majami'u da masallatai ya haifar da gagarumin ci gaba wajen gudanar aikin rigakafin corona cikin sauri a Kenya.

Shafin jaridar The Star ta kasar Kenya ya bayar da rahoton cewa, a farkon watan Disamba, Ma'aikatar Lafiya ta Kenya ta shiga wani aiki na hadin gwiwa da majami'u da masallatai da za a yi amfani da su a matsayin cibiyoyin rigakafin Covid-19.
 
Wannan mataki ya biyo bayan nuna damuwa ne game da rashin karbuwar allurar rigakafin a tsakanin jama’a, musamman a garuruwan yammacin kasar da kuam tsakanin mutane tsofaffi.
 
Hukumomin lafiya na Kenya sun ce hakan ya faru ne saboda rashin fahimta da kuma yada jita-jitar cewa rigakafin Covid-19 yana hana haihuwa, amma amfani da wuraren ibada a Kenya ya inganta tsarin rigakafin.
 
A cewar shugaban hukumar rigakafi ta Kenya Willis Akhwale, aikin rigakafin ya inganta cikin kwanaki 10 da suka gabata bayan daukar wannan mataki na hada kai da majami’u da kuma masallatai.
 
A Kenya, shugabannin addinai yanzu suna kaddamar da wani kamfen na wayar da kan dukkanin al'ummomi mabiya addinai game da bukatar yin rigakafin Covid-19.
 
An kaddamar da gangamin ne tare da gwamnati, da kungiyar addinai ta Kenya da kuma UNICEF.
 
Ya zuwa yanzu, an yi wa mutane miliyan 9.8 allurar rigakafin a fadin Kenya, daga cikin wadannan mutane, miliyan 5.7 sun sami kashi na farko, yayin da miliyan 4.08 suka sami cikakkiyar allurar rigakafin.

 

4025098

 

 

captcha