IQNA

OIC Ta Goyi Bayan Kawo Karshen Matsalar Sudan Ta Hanyar Tattaunawa

15:54 - January 10, 2022
Lambar Labari: 3486801
Tehran (IQNA) Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi maraba da sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na gudanar da tattaunawa tsakanin bangarorin siyasar Sudan.

A cikin wata sanarwar manema labarai da sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya fitar, ya jaddada goyon bayan kungiyar ga shawarwari da bangarori na kasa da kasa suka gabatar domin cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin Sudan, da fifita muradun al'ummar kasar maimakon muradu na daidaikun mutane, da kuma samar da zaman lafiya, dimokuradiyya, tsaro da cigaba.

A cikin wannan sanarwa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Hussein Taha, ya jaddada goyon bayansa ga kasar Sudan, domin tabbatar da tsaronta, da zaman lafiyarta, da hadin kan kasa, da wadata, da kuma kudurin da ta dauka na yin amfani da dukkan karfinta wajen aiwatar shirin da aka sanya a gaba na mika mulki ga farar hula.

A ranar Asabar 18 ga watan Disamba, wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya wadda za ta taimaka wa shirin mika mulki a kasar Sudan (UNITAMS) ta sanar da fara gudanar da cikakken tsarin tattaunawa don cimma yarjejeniyar kawo karshen rikicin siyasa a Sudan.

Shafin sadarwa na yanar gizo na UNITAMS ya bayyana cewa, wakilin musamman na babban sakataren MDD, kuma shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD Volker Pertz, ya fara tuntubar dukkanin bangarorin siyasa na Sudan da na kasa da kasa, wanda majalisar dinkin duniya ta dorawa alhakin gudanar da wannan aikin, domin kawo karshen rikicin siyasar da ake fama da shi a yanzu a Sudan, domin samun ci gaba mai dorewa zuwa ga dimokradiyya da kuma zaman lafiya a kasar.

 

 

4027575

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha