IQNA

Al-Azhar ta yi Allah wadai da hare-haren ta'addanci a Najeriya

18:46 - January 10, 2022
Lambar Labari: 3486802
Tehran (IQNA) Al-Azhar ta yi Allah wadai da hare-haren ta'addanci a arewacin Najeriya tare da jajantawa jama'a da gwamnatin kasar.

Shafin yada labarai na Almisrawi ya habarta cewa, cibiyar Al-Azhar Al-Sharif ta yi  Allah wadai da hare-haren ta'addanci a arewacin Najeriya tare da jajanta wa tarayyar Najeriya da jama'ar da abin ya shafa.

An kashe fararen hula 200 da ba su ji ba ba su gani ba a hare-haren ta’addanci da ‘yan bindiga suka kai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Azhar a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau litinin inda ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa wadanda ba su ji ba ba su gani ba, yana mai cewa: Yaki da ta'addanci na bukatar kayan aiki da taimako na kasa da kasa.

A karshen sanarwar, Al-Azhar ta nuna matukar damuwarta da jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa da kuma al'ummar Najeriya, tare da addu'ar Allah Madaukakin Sarki da ya bayar da sauki ga wadanda suka jikkata cikin gaggawa, ya kuma kawo zaman lafiya a duniya baki daya.

 

 

 

4027717

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: arewacin Najeriya ، cibiyar Azhar ، Allah madaukakin sarki ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha