IQNA

Wata kotun daukaka kara a Saudiyya ta tabbatar da hukuncin kisa kan wasu matasa biyu 'yan kasar Bahrain

22:48 - January 11, 2022
Lambar Labari: 3486808
Tehran (IQNA) Wata kotun daukaka kara a kasar Saudiyya ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa wasu matasan Bahrain biyu da ake zargi da aikata zagon kasa a kasar.

A yau Talata ne wata kotun daukaka kara a kasar Saudiyya ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa wasu matasan Bahrain biyu.

Matasan na Bahrain Jafar Sultan da Sadegh Thamer, mazauna yankin Katif ne, an kama Sultan da Thamer a shekara ta 2015 bisa zargin kokarin tarwatsa mashigar sarki Fahd da ke hada Saudiyya da Bahrain.

Su biyun dai na da kasa da wata guda domin su daukaka kara kan hukuncin zuwa kotun kolin Saudiyya.

Don haka a cewar rahoton, idan har kotun kolin Saudiyya ta amince da hukuncin, to dole ne ma sarkin Saudiyya ya amince da hukuncin kisa.

Sai dai matasan Bahrain biyu sun musanta wannan zargi tare da jaddada cewa zargin siyasa ne kawai saboda banbancin mazhaba.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa sun sha bayar da rahoton azabtarwa da aka yi wa matasan biyu, inda kungiyoyin ke cewa  jami’an tsaron Saudiyya na azabtar da su ne domin su amince da tuhumar da ake musu da kuma tilasta musu yin ikirari da laifin da ba su aikata.

 

4027977

tilasta

captcha