IQNA

Mahmoud Shahat yayi koyi da karatun mahaifinsa

Tehran (IQNA) Mahmoud Shahat Anwar matashin makaranci dan kasar Masar, ya karanta ayoyin kur'ani mai tsarki tare da koyi da mahaifinsa a tashar talabijin ta Al-Nahar ta kasar.
Mahmoud Shahat ya karanta suratul Hamd a cikin koyi da mahaifinsa a cikin wannan shiri da aka gudanar a kan cika shekaru goma sha hudu da rasuwar mahaifinsa "Shahat Mohammad Anwar" a tashar tauraron dan adam ta "Al-Nahar".
 
Shahat Muhammad Anwar ya kasance daya daga cikin fitattun mahardata kur’ani na kasar Masar, har aka rika kiransa da Akbar al-Qura makaranta na zamaninsa.
 
An haife shi a Masar a ranar 1 ga Yuli, 1950, kuma ya rasu a ranar 13 ga Janairu, 2008 yana da shekaru 58.