IQNA

Tatashar Talabijin Din Isra'ila Na Shirin Bude Ofisoshi A Morocco Da Bahrain

22:11 - January 12, 2022
Lambar Labari: 3486813
Tehran (IQNA) Tashar talabijin din Isra'ila ta I24 News na shirin bude ofisoshi a Bahrain da Morocco bayan bude ofishi a Dubai.

Jaridar Les Echos ta kasar Faransa ta rawaito cewa tashar i24NEWS ta  Isra'ila tana ci gaba da kokarin bude ofisoshi biyu a Bahrain da Morocco.

Jaridar ta ruwaito Jerome Bourdon, farfesa a fannin sadarwa a jami'ar Tel Aviv yana cewa i24NEWS wata hanya ce wacce ke dinke barakar da ke tsakanin aikin jarida da farfaganda da nufin daukaka matsayin Isra'ila.

Masanin ya jaddada cewa wannan tasha tana yin watsi da bayanai masu tada hankali kamar laifukan da yahudawa 'yan mamaya ke aikatawa.

A cikin watan Disamba 2020, Shugaban tashar Frank Moll, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tare da Kamfanin Media na Abu Dhabi, bayan haka ya sanya hannu kan wasu kwangiloli tare da Ofishin Watsa Labarai na  Dubai, Etisalat, Golf News, da Motivation Media da Intermedia.

Tashar i24News cibiyar sadarwa ce ta sa'o'i 24 da ke watsa shirye-shirye cikin Ibrananci, Ingilishi, Larabci, Sifananci da Faransanci.

 

4028147

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha