IQNA

Morocco: Mutane sun yi kira da a mayar da kwafin kur'anai a masallatai

21:32 - January 13, 2022
Lambar Labari: 3486818
Tehran (IQNA) 'Yan kasar Moroko da masu fafutuka sun yi kira ga ma'aikatar da ke kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar da ta mayar da kwafin kur'anai da aka karba daga masallatai saboda tsaftar muhalli.

Masu fafutuka a kasar Morocco a cikin shafin Facebook sun yi kira ga ma'aikatar da ke kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar da ta mayar da kwafin kur'anai da aka kwashe daga masallatai na kasar.

“An sake bude masallatan ne ‘yan watannin da suka gabata, amma ba a yarda a mayar da kwafin kur’ani zuwa wadannan wuraren ibada ba,” in ji Abdul Samad Mukhlis mai fafutuka a kasar Morocco.

Ya kara da cewa: “A yanzu an tilasta musu da su kawo Alkur’ani daga gidajensu zuwa masallatai ga duk wanda ke buktar yin karatu, ko kuma su rika amfani da wayoyinsu wajen karatun Alkur’ani.

A daya bangaren kuma shugaban kungiyar raya tattalin arziki da zamantakewa ta kasar Morocco Abdul Ali Al-Rami ya yi kira ga ma’aikatar da ke kula da harkokin raya kasa da ta mayar kur’anai a masallatai da sauran wuraren ibada na addini.

 

4028347

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha