IQNA

An Kawo Karshen Matakin Sharar Fage Na Gasar Kur'ani Ta Kasa Da Kasa A Iran

19:10 - January 16, 2022
Lambar Labari: 3486829
Tehran (IQNA) an kawo karshen matakin sharar fage na gasar kur'ani ta kasa da kasa a Iran

A yammacin yau ranar 16 ga watan Janairu ne aka kammala matakin share fage na gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 38 na Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da tantance mahalarta taron ga kwamitin alkalai.

A matakin farko na gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da ake gudanarwa a kasar Iran, maza daga kasashe 42 a fannin karatu na bincike, maza daga kasashe 40 a fannin hadda da ilmin tafsir, maza daga kasashe 23 a fannin karatu da harda.

Jimlar mahalarta 190 daga kasashe 69 za su kasance a cikin dukkan fannoni da sassan a gasar ta wannan shekarar.

 

4028777

 

captcha