IQNA

Masallacin Istiklal, Masallaci mafi girma a kudu maso gabashin Asia

Tehran (IQNA) Masallacin Istiqlal dake babban birnin Jakarta na kasar Indonesiya shine masallaci mafi girma a yankin kudu maso gabashin Asiya wanda ke da damar karbar masu ibada 120,000.

An kaddamar da masallacin na musamman ne a shekarar 1978 bayan shafe shekaru 17 ana gine-gine domin tunawa da zagayowar lokacin da kasar ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Holland.